Abdul’aziz Ganduje Ya Koma Bangaren Shekarau G7

Alfijr

Alfijr ta rawaito, babban Ɗan gwamnan kano, Abdul’aziz Abdullahi Umar Ganduje, ya koma bangaren tafiyar tsohon gwamnan kano Mal.Ibrahim Shekarau da akewa laƙabi da G7 tare nuna rashin gamsuwarshi akan yadda ake tafiyar da al’amurran gwamnatin a jihar.

Alfijr

Tuni dai Abdul’aziz Ganduje ya kai ziyarar mubaya’a ga Sanatan mazaɓar kano ta Arewa Sen. Barau I. Jibrin a gidan shi da ke jihar kano.

Idan baku manta ba a ƙwanakin baya dai Abdul’aziz Ganduje ya kai ƙarar mahaifiyarsa Prof. Hafsat Ganduje inda ya aikewa da hukumar yaƙi da masu yi ma tattalin arziƙin kasa ta’annati EFCC wasiƙa domin bincikarta akan zargin badaƙalar waɗansu filaye da kuɗaɗe.