Yadda Jama’ar Gari Sun Kona Wasu Masu Kwacen Waya Da Ransu

Alfijr

Wuta
Hoto Daga Premium Times

Alfijr ta rawaito wani ganau ya shaida cewa mutanen su uku sun zo ne a cikin babur mai kafa uku suka kwace wa matar waya da jakar hannu a bainar jama’a a garin Anaca, Jihar Anambra.

Alfijr

Masu kwacen nan suka yi wa matar kwacen waya da jakar hannunta, sannan suka koma suka shiga babur dinsu za su gudu, cikin taimakon babur din ya ki tashi.

Nan take wasu matasa da ke lodin motoci da sauran mutane dake wajen suka yi musu tara tara, suka kama su tare da fara dukansu, wasu suka debo tayoyi, wasu kuma fetur aka bulbula musu, aka cinna musu wuta da ransu, amma daya daga cikinsu ya ranta a na kare.

Alfijr

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar al amarin.

Ikenga, ya ce, ’yan sandan da aka tura bayan faruwar lamarin sun yi kokarin kwantar da kurar.

Ita kuma matar da aka yiwa kwacen an mayar mata wayarta da jakarta, babur din kuma na barayin wayar jama an tsaro sun tafi dashi.

Alfijr

Kakakin ya bayyana cewa ’yan sanda za su ci gaba da neman daya barawon wayar da ya tsere don girbar abinda ya shuka.

Kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito

Slide Up
x