Gobara ta Lakume kayayyakin Sama da Miliyan N18m A Dakin Ajiyar SEMA, A jihar Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito, wata gobara da ta tashi da yammacin ranar Juma’a a dakin ajiyar kayan agajin gaggawa na jihar Kano (SEMA), ta lalata kadarori na Naira miliyan 18.5 a unguwar Marie karamar hukumar Kumbotso.

Alfijr

Sakataren zartarwa na hukumar SEMA, Dr Saleh Jili, ya tabbatar da faruwar hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Juma’a.

Ya ce lamarin ya afku ne a ranar Juma’a da misalin karfe 1 na rana a dakin ajiyar SEMA na Mariri inda suka cika makil da kayayyakin agajin gobara da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.

Alfijr

A cewarsa, a makarantar First Lady da ke kusa da wajen ajiyar hukumar sune ke kone wani daji wanda sanadin hakan gobarar ta tashi har ta shafi dakin dalibai uku da suka kone kurmus.

Kayayyakin da suka lalace sun hada da katifa 450, matashin kai 450, katan 655 na Pampers na manya da yara.

Alfijr

Sauran kayayyakin da suka kone sun hada da katon Dettol guda 10, katan 10 na Omo, kwali 10 na Izal, injin nika, injin dinki, injinan Vulcanizing da gidan sauro, da dai sauransu, kudinsu ya kai Naira miliyan 18.5.

Jili ya kara da cewa, jami’an mu za su tantance irin barnar da aka yi da kuma kudin da za a biya don mikawa ga gwamnati don taimako.”

Ya yi kira ga jama’a da hukumomin makaranta da su yi taka tsantsan wajen kona daji.

Alfijr

Jili ya shawarci mazauna garin da su kasance da dabi’ar kashe kayan wutar lantarki a lokacin da za su fita daga gidajensu ko kuma kafin su kwanta barci.

Kamar yadda NAN suka rawaito