Kotu ta Aike Da Sadiya Haruna Gidan Gyaran Hali Da Tarbiyya

Alfijr

Alfijr ta rawaito kotun Majisitiri da ke filin jirgin saman Mal Aminu Kano ta yanke hukunci ɗaurin watanni shida ba tare da zaɓin tara ba ga Jaruma Sadiya Haruna

Freedom radio ta sanar da zaman kotun na yau Mai Shari’a Muntari Garba Ɗandago ya yanke mata wanann hukuncin ne bisa kalaman ɓatanci da ta yi ga wani mai suna Isah I. Isah a shafinta na social media Instagram.

Alfijr

Idan zaku iya tunawa dai a shekarar 2019 aka samu saɓani tsakanin Sadiya Haruna da Isah I Isha.

Daga nan ne kuma ta yi masa kakkausan kalamai a cikin wasu faya-fayan bidiyo da ta riƙa wallafawa.

Alfijr

Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan da Sadiyan ta sanar da cewa wasu na ƙoƙarin yin garkuwa da ita har office dinta.

Sadiya Haruna ta yi fice a kafafen sada zumunta wajen siyarda maganin maza da na mata da kuma yawan cece-kuce a shafinta.

Alfijr

Ko a shekarar da ta gabata wata kotun ta yanke mata hukuncin komawa makarantar Islamiyya bayan da Hisbah ta zarge ta da bayyana tsiraici da sakin baki a kafafen sada zumunta.

Slide Up
x