Alfijr
Alfijr ta rawaito, wani bincike da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gudanar ya nuna cewa, kanin tsohon shugaban kungiyar ‘Intelligence Response Team’ (IRT), Abba Kyari, ya karbi ₦235,120,000 daga hannun dan damfara ta intanet, Ramon Abass wanda aka fi sani da Hushpuppi.
Alfijr
Jaridar Trixxng.com ta bayyana rahoton na ‘yan sandan ya kuma bayyana yadda mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar ya karkatar da naira miliyan 44 zuwa asusun bankin dan uwansa a wasu mu’amala da su, rahoton bai bayyana ko kanin dan sandan da aka dakatar yana aiki ne a matsayin wakili ga Kyari ba.
A yanzu haka hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA tana tsare da shi.
Alfijr
Rahoton binciken da aka mika wa Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami, ya bayyana cewa, dan’uwan Kyari ya karbi jimillar kudi miliyan N279.120 daga wata kungiya ta yanar gizo kamar Efe Martins (jagora ko’odineta), Sikiru Adekoya, Usman Ibrahim, da kuma Hussaini Ala.
Duk da haka, ya kasa bayar da cikakken bayani kan me ake nufi da kudaden da kuma abin da ya yi da kudaden.
Alfijr
Kamfanin sadarwa na Hushpuppi Internet fraud Syndicate ya kunshi Efe Martins a matsayin babban kodinetan wanda ta hannun kamfaninsa Efe Martins Integrated Concept Ltd. a lokuta daban-daban ya mika makudan kudade daban-daban ga Sikiru Adekoya, Usman Waziri Ibrahim, Hussaini Ala. Dan uwa DCP Kyari babban mai cin gajiyar kudi ne daga asusun Zenith Bank na Hussaini Ala inda a lokuta daban-daban ya karbi kudade daban-daban da suka kai N218, 120, 000.
Ya kuma karbi N44m a wasu mu’amala da suka yi daga hannun DCP Abba Kyari.
Alfijr
Kwamitin ladabtarwa na rundunar a cikin shawarwarin da ya bayar kan rahoton binciken, ya tuhumi Kyari da laifin karya manufofin rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kafafen sada zumunta ta hanyar mayar da martani ga tuhumar da hukumar leken asiri ta tarayya ta yi a shafinsa na Facebook ba tare da gindaya wasu matakai ba.
Kwamitin ya tuhumi Kyari da yin karya da zamba, da kar ya ka’idojin sana’ar ‘yan sanda.
Alfijr
kwamitin ya yanke wa Kyari hukuncin rage daraja daga DCP zuwa ACP, tare da bayyana cewa “shaidar (N8mn) cin hanci yana da muhimmanci domin ba a biya mafi yawan cin hancin a asusun jami’in ba, haka kuma babu wani abin da aka samu na cin hancin da kwamitin ya binciko yadda ya rage alakanta jami’in da duk wani abu da aka samu.” FDC ta ci gaba da cewa, babu wata shaida da ke nuna cewa an tura kudade kai tsaye daga Hushpuppi ko Efe zuwa cikin asusun Kyari “amma akwai bayanan an karkatar da kudade daban-daban da suka kai N17m wadanda suka samo asali daga Efe Martins zuwa asusun Usman Waziri, Hussaini Ala da dan uwa DCP Kyari.”