Gaskiyar Magana Kan Auren Jaruma Aisha Tsamiya Da Hafsat Idris

Alfijr

Alfijr ta rawaito ɗaurin auren jaruma Aisha Aliyu Tsamiya gaskiya ne, an yi shine a sirri a kamar yadda aka saba na sauran jaruman ba.

Alfijr

“Aisha Tsamiya a ranar Laraba ta wallafa a shafinta cewa ba a ranar Juma’a (Jiya kenan) 25/2/2022 za a daura auren ta ba duk da cewa hakan yake a rubuce jikin wani katin gayyatar daurin auren da ya bayyana a kafafen sadarwa rubuce da inda za a ɗaura auren a masallacin Sheikh Zarban da ke Ƴan Kaba.”

Alfijr ta binciko cewa yadda labarin ɗaurin auren ya bazu tare da ɗaukar hankalin jama’a ganin cewa jarumar fitacciya ce sannan wanda za ta aura Alhaji Buba Abubakar shima babban mutum ne ya sa aka yi badda-sawu aka canza wurin ɗaurin auren.

Alfijr

“Daga ƙarshe dai an ɗaura auren jaruma A’isha Aliyu Tsamiya da Angon ta Alhaji Buba Abubakar a ranar Juma’a 25-02-2022 bayan boye boye da aka yi ta yi kan auren, amma an canja wajen ɗaurin Auren da lokacin da aka saka saboda dalilai na tsaro.

Alfijr

Kasancewar mijin Aishar babban mutum ne sananne, ita kuma fitacciyar jaruma ce wadda ke da ɗinbin masoya, dalilin haka ya sa aka hango matsalar da kuma muddin ana son kauce mata, to, dole a jirkita lamarin kamar yadda ya kasance, ba tare da an aiwatar kamar yadda aka tsara ba.

An dai ɗaura auren ne da safe a Masallacin Malam Aminu Ibrahim Daurawa.

Alfijr

Auren Hafsat Idris

Alfijr ta rawaito mai bada umarni a masa antar Kannywood Falalu Dorayi ya tabbatar mana da ɗaurin auren jarumar finafinan Hausa Hafsat Idris a ranar asabar a sirrince ce

Alfijr

Daga tsakargidan jaridar Alfijr Labarai muna taya jaruman murnar auren nasu Allah ya tabbatar da zaman lafiya.

Slide Up
x