Alfijr
Alfijr ta rawaito Tijjani Muhd Musa na cewa, yanzu dai k’watar waya da rana tsaka na nema ya zama ruwan dare a cikin al’umarmu, inda za ka ga matasa sun tari mace ko namiji da muggan makamai kai har ma da bindiga su ce a basu waya ko su kashe mutum.
Alfijr
Banda wannan yanzu abu ne da ba komai ba ka samu matasa da dududu ba su kai shekaru ashirin ba sun yi garkuwa da mutane wasu ma iyayensu, y’an uwansu, kannensu, makwabtansu da dai sauransu don neman kud’in fansa da sauran nau ikan laifuka da ake tafkawa a halin yanzu.
Duk kuwa ire-iren wad’annan abubuwan masha’a na faruwa ne mafi akasari saboda rashin aikin yi ko k’wad’ayin kudancewa ko ta yaya, da masu aikata hakan su ke yi.
Alfijr
INA MAFITA
- Dole a gina wani tsari mai dorewa na koyar da aiki ko sana’a a yayin da ake ilimantar da matasa, sannan yara tun suna kanana a fahimci abinda suka fi sha awa a dora su a kai.
- A samu wani k’wararre ko k’wararriya a dora musu nauyin koyar da yaro ko yarinya wannan aiki ko sana’a har sai ya ko ta iya shi sosai da sosai sannan a bada shaidar hakan wato kwalin satifiket.
- A bawa matashi ko matashiya damar nuna iyawarsa ko wani sabon salon fahimtarsa wajen gudanar da aiki ko sana’ar da suka koya tun kafin ace sun fita daga hannu malamansu.
- Dole a koyawa yaran yadda za su nemi a biyasu a bisa tafarkin gaskiya da kyautata.
- Koyar da yin gaskiya a dukkan lamarin wad’annan matasa abu ne da ya kamata ya samu gurbin zama
- Bayan an tabbatar sun iya aiyuka ko sana’o’in nan, to a hada su wani ko wata da sa za su je su yi aikin tare da su na tsawon shekara biyu (2) cir kafin su kafa tasu, don samun karin kwarewa.
- A koyar da su haka kuma a basu k’warin gwuiwa wajen kafa tasu masana’antar wato in mutum ba zai iya yi shi kad’ai ko ita kad’ai ba toh su nemi wad’anda tasu ta zo d’aya su kafa kamfanin tare.
- A tabbatar an koya musu yin aikinsu bisa sahihanci ba tare da ha’inci, k’wange ko tauye mudu ba. Kuma ya zama daidai da yadda za a same shi da kyau da kark’o kamar na ko’ina a fad’in duniya (International Quality & Standard)
- In matasan nan sun gudanar da aikinsu kuma komai ya ji toh a biya su hak’k’in su ba tare da jinkiri ko b’ata lokaci ba kamar yadda Manzo SAWS ya yi umarni wato kafin gumin goshinsu ya bushe. $annan kar a tsintsinka musu kudinsu don kyashi da bakin ciki.
- Daga k’arshe dole hukuma ta tabbatar ba a zalunci mai gaskiya ba daga masu sana’ar har wad’anda suka ba su aikin. Duk inda aka samu matsala a nemi sulhu a daidaita tsakani kowa ya yi abinda ya dace a dora tafiyar cikin yarda da amincewa juna.
Alfijr
©2022 Tijjani M. M.
A Kiyayin Hak’k’in Mallaka