Gwamnati Ta Yi Amai Ta Kuma Lashe! Kan Umarninta Na Bude Jami’o’in Ƙasar

Alfijr ta rawaito gwamnatin tarayya ta janye umarninta na saka shugabannin Jami oi su bude makarantu don dalibai su ci gaba da karatu.

Alfijr Labarai

Tun da farko dai gwamnatin ta bada umarnin cikin wata wasika da Daraktan Kudi na Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC), Sam Onazi, ya aike wa jami’o’in tarayya, a madadin Shugaban hukumar, Farfesa Adamu Rasheed.

A cikin wasikar dai gwamnati ta umarci shugabannin jami’o’in su tabbatar malamai sun koma aiki gadan-gadan domin harkokin koyo da koyarwa su ci gaba a makarantun Kasar.

Sai dai daga bisani an janye umarnin a cikin wata sabuwar wasikar mai lamba, NUC/ES/138/Vol.64/136, wacce ita ma Sam Onazin ya rattaba wa hannu.

Alfijr Labarai

Kakakin hukumar NUC, Haruna Lawal Ajoh, ya ce an janye umarnin ne saboda wanda ya rattaba mata hannu mukaddashi ne ba shine ya kamata ya bada wannan umarnin ba.

Haruna ya kuma ce Ministan Ilimi da Shugaban NUC sun tattauna sannan sun amince da janye umarnin, domin har yanzu suna kan teburin sulhu ana tattaunawa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *