Alfijr ta rawaito kamfanonin Sufurin jiragrn sama a Nigeria zasu tsayar da zirga zirgarsu daga ranar litinin Mai zuwa sakamakon yadda farashin man da suke amfani dashi yayi tashin gwaurin zabi a kasar
Wata sanarwa da kamfanonin suka rabawa manema labarai, ta bayyana cewa yanzu kamfanonin na sayen man da jirgin sama ke amfani dashi akan naira 700 duk lita 1
Manyan kamfanonin Sufurin jiragen sama a Nigeria ne suka amince da daukar matakin, cikin su kuwa har da azman airline da ibom airline sai Kuma arik da sauransu.
Alfijr
Masana na ganin Gwamnatin Tarayya ta Gaza shawo kan matsalolin, duba da yadda aka kasa warware matsalar fetur da gas suka gaza wadata Yan Nigeria.
Abin jira agani shine yadda wannan yajin aiki na jiragen sama zai shafi Fannin Sufurin Nigeria idan Gwamnatin Tarayya ta Gaza shawo kan matsalar