Makarantar Maryam Abacha (MAAUN) Ta Nada Babban Limamin Jami ar Na Kano

Alfijr ta rawaito Sheikh Hassan shine limamin gidan marigayi Janar Sani Abacha dake kan titin Gidado, Nassarawa GRA, Kano.

An haifi Sheikh Hassan a garin Gamborin Gala da ke jihar Borno a shekarar 1966,ya kamalla karatun kur’ani a shekarar 1972 sannan ya kammala haddar kur’ani a shekarar 1985.

Haka nan a shekarar 1991 ya sake rubuta Al-Qur’ani da hannunsa sannan a 2018 ya halarci wani taro. na Manyan Limamai na Masallatan Juma’a na kasar Morocco.

Alfijr

Bukatar nadin Sheikh Hassan a matsayin Babban Limamin Masallacin Juma’a na MAAUN na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan Talata 3 ga watan Mayu, 2022, mai dauke da sa hannun Hajiya Maryam Abacha, kuma aka rabawa manema labarai a Abuja ranar Laraba.

Dakta Maryam Abacha ta bayyana a cikin wasikar cewa, bukatar ta taso ne a kan cewa Sheikh Hassan yana da ilimin addinin Musulunci da ake bukata da kuma cancantar gudanar da Sallah a Masallacin duba da kasancewarsa mai haddar Al-Qur’ani kuma amintacce.

Alfijr

A cewarta, Sheikh Hassan yana da ilimin da ake bukata a fannin Fikihu, Shari’a da kuma iya harshen Larabci.

Don haka muna so mu tabbatar wa duniya cewa Sheikh Muhammad Hassan shi ne babban limamin masallacin Juma’a na MAAUN Kano, muna taya shi murna da farin ciki tare da yi masa fatan shiriyar Allah, in ji Maryam Abacha a cikin wasikar.

Slide Up
x