Kasar Saudiyya Ta Ankarar Da Musulmin Duniya Yadda Zasu Gane ZamZam Na Jabu Da Aka Fito Dashi

Alfijr ta rawaito ƙasar Saudiyya sun ɗauki mataki na magance yaɗuwar ruwan ZamZam na jabu a ƙasashen duniya.

Sakamakon rahotannin baya-bayan nan na gurbataccen kwalabe na ZamZam a sassa daban-daban na duniya da suka yadu hukumomin kasar sun fito da yadda robobin ZamZam na gaske suke don gujewa na jabu.

Alfijr

Alfijr

Wadannan sune hotuna daga kwalabe na gaske wanda ke nuna cewa ZamZam na gaske ne.

Kamar yadda shafin Haramain ya wallafa a Twitter.