Kungiyar ASUU Ta Bayyana Ali Isah Fantami A Matsayin Farfesan Bogi

Alfijr

Alfijr ta rawaito, ASUU) ta ki amincewa da karin girma ga ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Ibrahim Pantami a matsayin Farfesa a fannin tsaro na yanar gizo da hukumomin jami’ar fasaha ta tarayya, Owerri (FUTO) suka yi.

Alfijr

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a wani taron manema labarai a Lagos a karshen taron kwanaki biyu na majalisar zartarwa ta kasa (NEC).

Ya bayyana karin girma a matsayin ‘haramtacciyar doka.

Alfijr

Shugaban ASUU ya ce: “Yan uwa ‘yan jarida, za ku iya tuna cewa kungiyarmu ta ware kanta daga nadin Dr Ibrahim Pantami a matsayin farfesa a fannin tsaro ta yanar gizo da Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri (FUTO) ta yi a yayin taron mu na NEC da aka gudanar a Jami’ar. na Abuja a ranakun 18-19 ga Nuwamba, 2021,. har sai wata tawagar binciken gaskiya da za a aika zuwa reshen ta bayar da rahoton binciken ta.

Tawagar ta ziyarci reshen ne a tsakanin ranakun 10-14 ga Fabrairu, 2022, kuma ta kai rahoto ga Hukumar NEC. Sakamakon cikakken rahoton da aka gabatar a kan dukkan abubuwan da suka dace.

Alfijr

Daga shaidun da muke da su, Dokta Pantami bai cancanta ba, kuma nadin da aka yi ya saba wa ka’idojin da aka kafa na nadin malaman jami’a.

NEC ta umurci daukacin mambobin kungiyarmu da rassan kungiyarmu a fadin tarayyar Najeriya da kada su amince, ko kuma su dauki Dokta Isah Ali Ibrahim Pantami a matsayin farfesa a harkar tsaro ta yanar gizo ta kowace hanya.

Alfijr

“NEC ta kuma kuduri aniyar hukunta duk ‘yan kungiyar ASUU da suka shiga aikin wanda ya kai ga nadin ba bisa ka’ida ba bisa ka’idojin kungiyar mu.”

Slide Up
x