Matashin Da Ya Ƙirkiri Mota Mai Amfani Da Lantarki A Barno, Ya Shiga Kundin Tarihi

Alfijr ta rawaito mataimakin Shugaban Ƙasa, Osinbajo Ya Karrama matashin da da kirkiri wata mota mai amfani da lantarki da lambar yabo ta Musamman

Alfijr Labarai

Mustapha Gujibu wani gasihin matashi ne ɗan asalin jihar Borno, wanda Allah ya bawa bazaar kirkira har ya ƙirkiro mota mai amfani da wutar lantarki, dalilin wannan bajintar ta sa aka gwamna Baba Zulum yana yaba masa.

Baya ga nan kuma mataimakin shugaban Farfesa Yemi Osibanjo, ya karrama shi da wata lambar yabo.

Haka zalika, Gwamnan jihar Borno Umar Babagana Zulum, ya gwangwaje matashin da kyautar kuɗi Naira Miliyan daya domin ƙarfafa mashi gwiwa. 

Alfijr Labarai

A halin yanzu dai kamfanin (Nigerian Automotive Design and Development Council (NADDC) Wanda Jelani Aliyu ke shugabanta sun dauki yaron aiki domin bashi kwarin guiwa wajen ciyar da Najeriya gaba.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *