Mutane Biyar Sun Sake Mutuwa An Kuma Ceto 4, A Wani Hatsarin Kwale-kwale Da Ya Afkuwa.

Alfijr ta rawaito wani sabon Hadarin Jirgin ruwa ta sake faruwa a karamar hukumar Gwaram.

Alfijr Labarai

Hakan na zuwa ne kasa da mako guda da wani kwale-kwalen ya yi hatsari a karamar hukumar Miga, inda matasa biyu suka mutu lokacin da suke kan hanyar su ta dawowa daga gona, ƴan Sandan jihar sun tabbatar da faruwar lamarin,

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Lawan Ahmad ne ya shaida wa jaridawa manema labarai cewa, hatsarin baya-bayan nan mutanen na dawowa daga sallar Juma’a, lokacin da sukai hatsarin.

Binciken da Alfijr ta yi, ya tabbatar da cewa, ana dora mutane fiye da kima, da rashin rigar kariya idan hatsari ya afku a cikin

Alfijr Labarai

Lawan ya kara da cewa “Mutane biyar ne suka mutu, an kuma yi nasarar kubutar da mutane hudu a a hatsarin.

Lamarin ya faru ne da rana misdalin karfe biyu na rana, kuma jirgin ruwan na dauke da fasinjoji tara lokacin da lamarin ya faru, in ji Lawan.

Slide Up
x