Rundunar Sojin Najeriya Ta Sake Kama Wani kasurgumin Dan Ta’adda

Alfijr ta rawaito rundunar sojin Najeriya ta sake kama wani kasurgumin dan ta’addan da aka dade ana nema ruwa a jallo

An kama Modu Babagana ne a karo na biyu bayan ya tsere daga gidan gyaran halib da aka ajiye shi a shekarar 2020

A yanzu da aka sake kama shi, an kama shi ne lokacin da yake siyayya ga ‘yan ta’addan Boko Haram

Alfijr

Dakarun runduna ta musamman ta 21 dake garin Bama aa jihar Borno sun kama kasurgumin dan leken asiri da ake nema ruwa a jallo na ‘yan ta’addar Boko Haram/ISWAP, Modu Babagana, wanda ya tsere daga hannun sojoji a garin Bama ta jihar Barno.

An kama fitaccen dan ta’addan ne a baya a watan Janairun 2020 da laifin aikita leken asiri kan sojoji a yankin Bama da Banki.

Kamar yadda Leadership ta wallafa

Slide Up
x