Rundunar ‘Yan Sandan Ta Dakile Wani Hari Da ‘Yan Fashi Da Makami Suka kai Wata Kasuwa

Alfijr ta rawaito rundunar ƴan Sandan jahar Delta ta kwato bindigogi kirar AK47, da harsashi 9mm, a wani mataki na gaggawa da jami’an rundunar suka dauka na dakile wani harin ‘yan fashi da makami da aka shirya kai wa a kasuwar Hausa dake Asaba babban birnin jihar.

Alfijr Labarai

Jami’an ‘yan sanda daga CP’s Decoy Squad sun amsa kiran gaggawa lokacin da aka ga wasu mutane da ake zargi da ke kan babur din adaidaita sahu a yankin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ga manema Labarai.

Ya ci gaba da cewa, “A ranar 11/09/2022 da misalin karfe 04:30 na safe, rundunar ‘yan sandan ta yi gaggawar amsa kiran kasuwar Hausawa da ke Asaba, kan wasu mutane da ake zargi da amfani da babur din adaidaita su uku a yankin, jami’an rundunar ‘yan sanda ta CP-Decoy Squad.

‘Yan bindigar da suka hango ‘yan sandan suka yi watsi da adaidaitan suka ranta a na kare.

Alfijr Labarai

“A binciken da aka yi wa babur din, an gano bindiga kirar AK 47, harsashi guda goma sha biyu (12) kirar 9mm da harsashi guda ashirin da uku (23) wadanda aka boye a cikin bakar jakar polythene da aka boye a karkashin kujerar fasinja ta baya.

“An kara kaimi tare da hadin gwiwar ‘yan banga na cikin gida domin kamo wadanda ake zargi da gudu.”

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ari Muhammed Ali, ya yaba da kokarin mazauna jihar wadanda koda yaushe suka taimakawa rundunar da bayanan da ke taimakawa wajen yaki da miyagun laifuka.

CP ya kuma bukace su da su ci gaba da bayar da hadin kai da Hukumar, tare da lura da cewa “laifi ba shi da hurumi, saboda masu aikata laifuka ba sa jin tausayin bil’adama don haka bai kamata a bar su su ci gaba da ayyukansu ba tare da hana su ba.

Alfijr Labarai

Ya kuma ba da tabbacin cewa duk wanda ya ba ‘yan sanda bayanai za a yi masa cikakkiyar godiya da kuma rufe sirrinsa

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *