Ana zargin ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Hon. Samaila Bagudo.
Rundunar ’Yan sanda ta tabbatar da cewa an sace dan majalisar ne a garinsu da ke Karamar Hukumar Bagudo, bayan ya idar da sallar Isha’i a daren Juma’a, 31 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 8:20 na dare.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya fitar, an bayyana cewa an tura hadakar jami’an tsaro da suka hada da rundunar ’yan sanda da sojoji da jami’an sa-kai domin ceto dan majalisar.
Sanarwar ta ce, “Jami’an tsaron hadin guiwa suna ci gaba da bincike a hanyoyin da ake zargin ’yan bindigar suke bi da dazukan da ke kewaye, domin ceto dan majalisar ba tare da wani rauni ba, tare da cafke wadanda suka aikata wannan aika-aika.”
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t