Wani Dan Kasar China Ya Kashe Wata Budurwa A Jahar Kano

Alfijr ta rawaito wani dan kasar Chinan dai na zargin Ummukulsum da yaudararsa, ta hanyar kin aurensa bayan ya Dade yana yi mata hidima.

Alfijr Labarai

Hakan ce ta Sanya ransa ya baciya kuma ya je har gidansu dake unguwar Yamadawa a Dorayi Babba ya kuma haura cikin gidan don aiwatar da mummunar manufarsa

Bayan ya haura ne ya shiga dakin yarinyar ta taga, ya zaro wuka ya fara caccaka mata a wuya da kafadunta.

Ko da ya kammala ya soka mata wukar ne sai ga mahaifyarta, ta yi ihun akawo taimako inda wami matashi ya yi kukan kura ya Kai dauki.

Kakakin rundunar yan sandan jihar kano Kiyawa yace, bayan samun Labarin ne kwamishinan yan sandan Kano ya tura jami’ansa karkashin DPOn Dorayi Babba CP Abubakar Lawan.

Alfijr Labarai

Ya ce da isarsu ne suka dauki yarinyar zuwa Asibitin Murtala inda likita ya tabbatar da da mutu.

Kiyawa ya ce tuni Suka damke wanda ake zargi kuma an mayar da shi shalkwatar Yan sandan domin ci gaba da bincike.

3 Replies to “Wani Dan Kasar China Ya Kashe Wata Budurwa A Jahar Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *