Mutane 7, Ne Suka Sake Mutuwa, Daya Kuma Ya Jikkata A Wani Gini Da Ya Rufta

Alfijr ta rawaito Mutane bakwai 7, ne suka mutu sannan daya ya jikkata a wani gini daya rufta a jihar Jigawa.

Alfijr Labarai

Kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar faruwar lamarin.

Shiisu ya ce ginin ya ruguje ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i ana yi.

Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar Asabar da misalin karfe 05:47, wani ginin laka ya rufta a kauyen Bursali karamar hukumar Birniwa ta jihar Jigawa.

Ya ce mutane bakwai ne suka mutu nan take yayin da mutum daya ya samu rauni.

Alfijr Labarai

Shiisu ya ce jami’an tsaro sun garzaya wurin da lamarin ya faru in da suka kai wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Birniwa nan take wani likita ya tabbatar da mutuwarsu.

Ya ce dayan wanda ya jikkata yana karbar magani.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *