Wani Matashi Ya Harbe Ƙaninsa Ya Tsere Abinsa A Jihar Kwara

Alfijr ta rawaito rundunar ƴan sandan Jihar Kwara, ta bayyana cafke wani matashi mai suna Abubakar bisa zarginsa da harbe ƙaninsa Yusuf ɗan shekera goma sha biyu lokacin da yake gwajin maganin bindiga a kansa.

Alfijr Labarai

Kakakin rundunar ƴan Sandan jahar SP Okasanmi ne bayyana hakan da ya fitar a ranar Litinin

SP Okasanmi, ya ce, rundunar ta ce ta cafke matashin ne bayan da ya gama guje gujensa yana buya.

Lamarin ya faru ne a garin Dutse Gogo da ke yankin ƙaramar hukumar Kaiama a ranar Lahadin da ta gabata.

Haka kuma ta ƙara da cewa afkuwar lamarin ya janyo mazauna yankin sun shiga halin firgici da jimami.

Alfijr Labarai

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *