Wani Yaro Dan Shekaru Uku Ya Harbe Mahaifiyarsa Har Lahira

Alfijr

Alfijr ta rawaito wani yaro mai shekara uku ya harbe mahaifiyarsa har lahira bisa kuskure, yayin da yake wasa da wata bindiga a wajen birnin Chicago, kamar yadda ‘yan sanda suka sanar.

Wannan abin takaicin ya faru ne ranar Asabar da karfe 8:30 na dare a wurin da ake ajiye motoci na wani katafaren shago, kamar yadda ‘yan sandan na yankin Dolton suka bayyana,

Yaron na zaune a kujerar baya ne, cikin motar mahaifinsa inda mahaifin nasa na zaune a kujerar direba tare da mahaifiyarsa a gaban motar, ba a san yadda yaron ya iya fito da bindigar ba, amma rahotanni na cewa ya rika yin wasa da ita ne a kujerar bayan motar.

Alfijr

Daga baya sai ya latsa kunamar bindigar kuma nan take harsashi ya fito kuma ya shiga ta wuyan mahaifiyarsa mai suna Deejah Bennett, inda ya kashe ta har lahira.

‘Yan sandan Dolton sun ruga da matar zuwa asibitin Jami’ar University of Chicago Medical Centre, sai dai likitoci sun ce ta riga ta cika.

Alfijr

Kamar yadda BBC Hausa Ta rawaito

Slide Up
x