Jarumi Umar Bankaura Yace Ku Sashi Cikin Addu’ar Sakamakon matsanancin Rashin lafiya

Alfijr ta rawaito tsohon ɗan wasan kwaikwayon nan Alhaji Umar Yahaya Malumfashi (Bankaura) ya bayyana cewa ya na buƙatar addu’a daga al’ummar Annabi saboda yanayin rashin lafiyar da ya ke ciki, wanda ya kai har an kwantar da shi tsawon lokaci a wani asibiti a Kano.

Alfijr Labarai

Dattijo Bankaura, wanda a yanzu ake kira Yakubu Ka-Fi-Gwamna saboda matsayin da yake takawa a diramar ‘Kwana Casa’in’ na gidan talbijin na Arewa24, ya na daga cikin daɗaɗɗun ‘yan wasan kwaikwayo da Arewa ke ji da su, domin ya fara dirama ne tun kafin a samar da masana’antar shirya finafinai ta Kannywood.

Alh Bankaura yana kwance ne a gidan sa da ke unguwar Hotoro Tsamiyar Boka daga bisani aka mai da shi wani asibitin kuɗi mai suna Pinnacle Special Hospital da ke unguwar Hausawa kusa da Masallacin Murtala in da ya ke kwance magashiyan.

Wakilin Mujallar Fim ta samu zantawa da shi a asibitin Daga kwance a gadonasibitin.

Alfijr Labarai

Bankaura ya faɗa wa wannan mujallar cewa: “Ka zo lokacin da ba zan samu damar da zan iya doguwar magana da kai ba saboda yadda na ke a yanzu, amma na gode da zuwan ka waje na.”

Duk da haka, ya ɗan yi bayanin cewa: “Na samu lokaci mai tsawo ba ni da lafiya, domin tun a watan Ƙaramar Sallah na ke cikin rashin lafiyar.

“Kuma dai ka ga a yadda ka same ni, kuma ina fatan ku ci gaba da yi mani addu’a; Allah shi ya san yadda zai yi da bayin sa.”

Alfijr Labarai

Haƙiƙa duk wanda ya san Bankaura, idan ya gan shi sai ya tausaya masa, domin ya na cikin yanayi na buƙatar taimako.

Allah ya ba shi lafiya, ya sa cutar ta zama kaffara a gare shi, amin.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *