Wata Sabuwa! Wutar Lantarki Ta Ƙasa Ta Lalace Gaba Ɗaya

Alfijr ta rawaito Layin wutar lantarki ta ƙasa ta sauka gaba ɗaya, ya kasance babu megawatts ko ɗaya, tun misalin karfe 10:51 na safiyar Litinin, lamarin da ya janyo katsewar wutar lantarki a fadin kasar baki daya.

Alfijr Labarai

Al amarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan da wutar ta fara damuwa a fadin kasar baki daya

Tashar wutar lantarki ta kasa da misalin karfe 10 na safiyar yau Litinin ta samu megawatt 3,712 da aka samar daga kamfanoni 21 na rarraba wutar lantarki (GenCos) kafin ta koma 0MW bayan awa daya.

Bisa ga bayanin da aka samu daga rumbin yaɗa bayanai na wutar lantarki, wani sashe na Kamfanin rarraba Wutar lantarki (TCN), Afam IV ne kawai a kan layin wutar, amma ba tare da an samu komai na wutar ba har zuwa karfe 12 na rana.

Alfijr Labarai

Yanzu haka ma aikatan kamfanin sun dukufa ka in da na in wajen magance matsalar

The PUNCH

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *