Yan bindiga Sun Buƙaci Naira miliyan 350 kuɗin Fansar Daractan APC Na Kasa.

FB IMG 1739361414670

Daga Aisha Salisu Ishaq

Ƴan bindigan da su ka sace Dakta Adekunle Raif Adeniji, Daraktan Gudanarwa na Sakatariyar  Jam’iyyar APC a Abuja, sun nemi a biya su kudin fansa Naira miliyan 350 kafin su sako shi.

Alfijir labarai ta rawaito cewa iyalansa sun samu kira daga masu garkuwar, inda su ka dage cewa sai an biya kudin fansa kafin su sake shi.

Wani daga cikin iyalansa, da ya yi magana da wakilin Daily Trust jiya Talata, ya ce Daraktan da wasu mutane da aka sace tare da shi suna hannun masu garkuwar har yanzu, kuma sun ce ba za su sake shi ba har sai an biya kudin fansar.

Wata majiya a APC ta tabbatar da wannan batu ga jaridar Daily Trust.

An sace Dr. Adeniji makonni biyu da su ka gabata a yankin Chikakore da ke Kubwa, cikin Ƙaramar Hukumar Bwari ta Babban Birnin Tarayya Abuja.

Daily Trust

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp 👇👇

https://chat.whatsapp.com/FNMJaJ3I8Sc0bkkm8aJQbQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *