Ƴan Bindiga Sun Kashe Wani DSP, Da Wasu ‘Yan Sanda 3 A Yayin Wani Farmaki

Alfijr ta rawaito Sama da Sa’o’i 24 Bayan Wasu ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mataimakin Sufeton ‘Yan Sanda (DSP) da wasu jami’ai uku; Hukumomin ‘yan sanda a Imo har yanzu ba su yi magana a kai ba.

Alfijr Labarai

DSP da wani Insifeto dake hedikwatar ‘yan sanda reshen Umuna da ke yankin Onuimo a jihar an bayyana cewa an harbe su ne a lokacin da suke tare da wasu kananan jami’an ‘yan sanda suka tsaya suna bincike a gaban hedikwatar ‘yan sandan shiyya ta.

Wasu rahototanni sun bayyana ƴan bindigar sanye da kakin soji kuma suna aiki a cikin wata bakar mota kirar Hilux, nan take suka abkawa jami’an.

Wata majiya mai tushe ta tabbatar da jami’an ‘yan sandan sun tare hanya ne da safe suna bincike.

Sai dai yan bindigar sun zo a bakar motar kirar Hilux dauke da mutane kusan biyar sanye da kayan Sojoji amma ba sojoji ba ne, ‘yan bindiga ne suka bude wuta kan jami’an ‘yan sandan da ba a san ko su wanene ba, inda suka kashe DSP da Insifeto sannan suka garzaya gaban sauran jami’an.

Alfijr Labarai

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto rundunar ‘yan sandan jihar Imo ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba duk da cewa jami’in hulda da jama’a, CSP Mike Abattam bai amsa kiran da aka yi masa ba a lokacin da aka tuntube shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Daily Trust

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *