Bayan Samunta Da Laifin Satar Miliyan 2.68 A Banki, Kotu Ta Daure Ta Shekaru 7

Alfijr ta rawaito babban alkalin kotun magistrate da take zamanta a Lagos, Kayode-Alamu ta yankewa Bassey hukuncin ne bayan gano shi da tayi, bayan da ya so yin basaja a matsayin Dan ba ruwana abaya

Alfijr Labarai

Ms Bassey, dai na daga cikin tsofaffun ma’aikaciyar bankunan, a wani binciken kwakawaf da aka gudanar a bankin an gano ta sace wasu kudaden da daga ranar 15 ga Afrilu zuwa 20 ga Afrilu a Iddo.

Kotun ta ce Laifin wanda ya sabawa sashe na 287(9) na dokar laifuka ta jihar Lagos na Shekarar 2015.

Sai dai wadda ake zargin Madam Bassey ta ki amsa laifin da ake tuhumarta da laifin sata a kotu a ranar 22 ga Afrilu.

Bayan dogon nazari da kotu ta yi akan shari ar, an bayar da belin ta a kan kudi N500,000 tare da mutane biyu masu tsaya mata, amma ta kasa cika sharuddan belin ta.

Alfijr Labarai

Sakamakon gaza cika wadannan sharudan aka aike da ita gidan gyaran hali na Ikoyi na tsawon watanni, kammala wannan hukuncin ne sai ta fadi gaban mai shari ar tana rokon sassauci.

Sakamakon haka ne kotun ta duba gaskiyar lamarin inda ta sake sassauta mata hukuncin.

Kotun ta ba ta zabi ta biya kudaden da ta sace a cikin shekara guda sannan ta yi zaman gidan yari na shekaru hudu a maimakon shekaru bakwai.

NAN

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *