Kotu Ta Daure Wasu Matasa Bisa Zargin Yin Zamba Da Batanci Da Sunnan Yar Sani Danja

Alfijr ta rawaito wata kotun Majistare mai lamba 47 da ke Kano ta ƙi ba da belin wasu matasa biyi nan da aka kama kan zargin su na amfani da sunan jarumar Kannywood Khadijatul Iman Sani Danja su na zambatar jama’a tare da yaɗa batsa a kafafen sada zumunta.

Alfijr Labarai

Ranar  Litinin ne aka sake gabatar da Jabir Muhammad da Abubakar Sunusi a gaban Mai Shari’a Hadiza Muhammad Hassan bisa tuhumar haɗa kai da ƙirƙirar labarin ƙarya da cin zarafi da kuma ɓata suna.

Jami’in kotun, Auwal Abdullahi, ya karanto musu laifikannsu, wanda hakan sun saɓa wa sashe na 97 da 324 da na 393 da kuma shashe na 392 na kundin Final Kod, sai dai wadanda ake zargin duk sun musanta aika laifukan.

Sai dai Lauyar gwamnati mai gabatar da ƙara, Barista Asma’u T. Gwarzo, ta buƙaci kotu da ta ba su wata ranar domin a sake gabatar da su, nan take kotun ta amince, inda ta aika da su zuwa gidan gyaran hali da tarbiyya zuwa ranar 27 ga Satumba, 2022.

Alfijr Labarai

A nata bangaren Jarumar kannywood dakan jiya wato  Mansurah Isah, ita ce ta kai su ƙara bisa amfani da sunan yarsu ita da Jarumi Sani Musa Danja suna batanci da sunan nata.

Bayan an fito daga kotun, an tattauna da lauya mai Kare mai kara, Barista Rabi’u Sidi, inda ya bayyana dalilin shari’ar da kuma inda aka tsaya.

Ya ce, “Ni ina tsaya wa Mansurah Isah ne a kan wannan ƙara inda mu ke ƙarar wasu mutane uku, Jabir Muhammad, Abubakar Sunusi, da kuma wani da har yanzu ba a kai ga kama shi ba, dangane da haɗa kai da su ka yi wajen buɗe shafuka na Facebook, Instagram, Twitter da YouTube inda su ka kira shafin da suna ‘Real Iman Sani Danja’ su na saka hotunan batsa, sannan su ka yi amfani da lambobin wayar su su na kiran wasu mutane su na karɓar kuɗaɗe a wajen su a matsayin ita ce. 

“Kuma sai binciken ya nuna an yi wannan abin domin ɓata wa ita Mansurah Isah suna da iyalan ta, don haka sai ta gabatar da ƙorafi a gaban ‘yan sanda na SIB kuma aka yi bincike aka kamo su.

Alfijr Labarai

“A yanzu ga shi an gabatar da su a gaban kotu, duk da cewa sun musa abubuwan da aka caje su da shi Lauyan su ya tashi ya nemi beli a gaban kotu, ta ce ta ɗaga sai ranar 27 za ta faɗi ra’ayin ta ko za ta bayar da belin ko ba za ta bayar ba.

“Don haka mu dai abin da mu ke nema ga kotu ta yi mana adalci a kan wannan shari’ar, domin akwai mutane da dama da su ke amfani da shafuka na manyan mutane su na ɓata musu suna tare da karɓar kuɗaɗe a wajen wasu da sunan su, don haka mu ke so kotu ta yi hukunci don ya zama izna ga yan baya.”

Fim Magazine

Slide Up
x

2 Replies to “Kotu Ta Daure Wasu Matasa Bisa Zargin Yin Zamba Da Batanci Da Sunnan Yar Sani Danja

    1. Don Allah kuyi afuwa Jamal idan kaga kuskure ba da gangan aka yi ba ajizanci ne kawai, amma za mu kara saka ido, muna godiya kwarai da kulawarku

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *