Kotu Ta Wanke Matar Wanda Ya Kashe Hanifa, Matar Ta Nemi Da Abdulmalik Ya Sauwake Mata

Alfijr

Alfijr ta rawaito jiya Juma’a ne aka sake gurfanar da Jamila, mai shekara 30 da haihuwa a Kotun Majistare 12 da ke gidan Murtala, bisa zargin haɗin baki da ɓoye marigayiya Hanifa.

Alfijr

Gurfanar da Jamila ya biyo bayan zaman da koti tayi a ranar Alhamis, Jamila ta baiyana a gaban babbar Kotun bisa jagorancin Mai Shari’a Usman Na-abba, ta bada shaida a kan yadda Tanko ya kawo Hanifa gidansa har ma ya yi ƙaryar cewa mahaifiyar yarinyar ce ta yi tafiya zuwa Abuja.

Alƙalin kotun, Muhammad Jibril, wadda aka sake gurfanar da Jamila a ranar Juma’a ya wanke ta ya kuma umarci da a sake ta da ga inda a ke tsareta tare da mijinta.

Alfijr

Bayan shakar is karta, ta zantawa da manema labarai, Jamila ta gode wa Allah bisa wanketa da akayi kuma ta ji daɗin irin adakcin da kotu tayi wajen tantance gaskiya.

Jamila Muhammad Sani, matar Abdulmalik Tanko, wanda aka zarga da yin garkuwa da kuma kashe Hanifa Abubakar a Jihar Kano, ta ce ta na son mijin nata ya rubuta mata takardar saki, ina neman miji na ya sake ni dan ba zan iya zaman jira ba

Alfijr

Ta ƙara da cewa, ni da har yanzu da ƙuruciya ta, ba zan iya zaman jiran sa ba, ni kawai ina neman ya sake ni in je in samu wani mijin na aura.

Slide Up
x