Gwamna Buni Ya Bawa Iyalan Sheikh Goni Aisamu Kyautar Gidaje 3 Da Tarin Kayan Abinci

Alfijr ta rawaito, wakilan Gwamna Mai Mala Buni sun dankawa wakilin iyalan Shaykh Goni Aisami mukullai da takardun gidaje guda uku.

Alfijr Labarai

Buni yace Kowacce daga matan Shaykh da ‘ya’yanta za su dau gida daya, cikin harda matarsa da suka rabu amma akwai ‘ya’ya tsakaninsu.

A baya gwamna yayi alkawarin sayawa iyalan Shaykh din gida, amma da ya tashi sai ya saya musu ba ma biyu ba, guda uku rinkis, haka kuma gwamnan ya cika alkawarin abinci da ya dauka.

Wakilai sun dankawa iyalan Shaykh Goni shinkafa buhu 12 da taliya katan 20 da mai jarka 5, sai kuma atamfa guda 10.

Daga karshe, hukumar ‘yansanda Jahar Yobe sun ce zuwa yanzu ba a gufanar da wadanda  ake zargi da yiwa Shaykh kisan gillar ba; hakan ya biyo bayan manya Kotuna suna hutu.

Alfijr Labarai

Amma tuni aka iza keyar zuwa gidan gyaran hali, kuma da Kotuna sun dawo za su gurfana gaban kuliya domin su girbe sharrin da suka shuka.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *