Gwamnatin Kogi Na Shirin Ƙwace Kamfanin Siminti Na Obajana Daga Hannun Dangote

Alfijr ta rawaito gwamnatin Kogi ta fara ɗaukar gaɓaran ƙwato kamfanin siminti na Obajana daga hannun kamfanin siminti na Dangote.

Alfijr Labarai

Kudurin gwamnatin na kunshe ne a cikin rahoton kwamitin kwararru na musamman don tabbatar da halascin mallakar kamfanin siminti na Obajana zuwa na Dangote daya fito a ranar Alhamis.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa an mika cikakken rahoton ga gwamna Yahaya Bello na Kogi a watan Satumba.

Sakatariyar gwamnatin jihar (SSG), Folashade Ayoade ce ta gabatar da rahoton a ranar Alhamis a Lokoja ga Gwamna Yahya Bello

Ayoade ta ce, ” ƙwato kamfanin siminti na Obajana Plc daga kamfanin Dangote Cement Company Limited ya zama wajibi a wannan lokaci.”

SSG ɗin ta gabatar da takardu cewa maida Obajana zuwa ga kamfanin Dangote “Ba halastacce ba, kuma rusasshe ne”.

Alfijr Labarai

Ta bayyana cewa a cikin rahoton, an nuna yadda a ka yi amfani da takaddun mallaka guda 3 na Kamfanin Simintin Obajana, mallakin gwamnatin Jihar Kogi, inda Dangote ya yi amfani da hakan ya ciyo bashin Nairq biliyan 63bn.

A cewarta, kwamitin bisa ga binciken da ya gudanar, ya bayar da shawarar cewa jihar Kogi ta dauki matakin kwato kamfanin siminti na Obajana daga hannun Dangote.

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

NAN

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *