Ibtila’i! Wasu Ƴan’uwa Biyu Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Rugujewar Wani Gini A Jihar Kano

Alfijr ta rawaito wasu ‘yan uwa biyu masu shekaru 15 da 11 sun mutu a ranar Juma’a sakamakon ruftawar wani bene mai hawa daya a jihar Kano.

Alfijr Labarai

Sanarwar ta ce, an ce an ceto babban dan uwansu mai shekaru 17 da rai.

Saminu Abdullahi, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar.

Ya ce gidan da ibtila’in ya faru yana unguwar Kofar Mata Hauren Gadagi a Kano.

“Mun sami kiran waya da misalin karfe 10:50 na dare daga wani Jamilu Salisu-Zango cewa ginin da aka yi amfani da shi a matsayin gida mai tsawon kafa 50 x 40 ya rushe daga bene,” in ji shi.

Alfijr Labarai

“Mun aika da tawagarmu zuwa wurin da lamarin ya faru kuma an fito da ’yan’uwan uku daga cikin tarkace.

Biyu daga cikinsu sun kasance a sume.”

Abdullahi ya kara da cewa an garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibitin Murtala Muhammad na musamman domin kula da lafiyarsu inda likitoci suka tabbatar da mutuwar ‘yan uwan ​​biyu.

Ya ce an mika gawarwakin ga ‘yan sanda yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Alfijr Labarai

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *