Shaaban Sharada Ya Nada Abbas Yushau A Kakakin Yakin Neman Zaben Gwamna

Alfijr ta rawaito dan takarar Gwamnan Jihar Kano A Jam’iyyar Action Democratic Party, Kuma Dan Majalisar Wakilai Na Mazabar birnin Kano ta Tarayya Shaaban Ibrahim Sharada Ya Amince Da Nadin Abbas Yushau Yusuf A Matsayin Kakakin Majalisar Yakin Neman Zabensa Gwamna.

Alfijr Labarai

A wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, a ranar Lahadi, dan takarar gwamna na jam’iyyar ADP, Shaaban Sharada, ya ce an nada Abbas Yushau Yusuf a matsayin Kakakin Yakin Neman Zaben ne saboda dimbin gogewar da yake da shi a harkar yada labarai da ya shafe sama da shekaru goma.

Dan takarar gwamnan ya bukaci sabon kakakin yakin neman zaben da ya kasance mai himma wajen tabbatar da ingantacciyar huldar yada labarai mai inganci da lafiya ba tare da nuna kyama ba.

Abbas Yushau Yusuf ya kammala karatunsa a Sashen Sadarwa na Jami’ar Bayero Kano a shekara ta 2008 kuma yana da gogewa a fannin bugawa, da kuma kafafen yada labarai na yanar gizo,” in ji sanarwar..

Alfijr Labarai

“Ya yi karatun digirinsa na biyu a tsangayar sadarwa ta Jami’ar Bayero Kano a shekarar 2016, kuma ya halarci kwasa-kwasai da karatuttuka da dama.”

A cewar sanarwar, Abbas ya kasance editan labarai a gidan rediyon Freedom, FM mai zaman kansa na farko a Kano, kuma ya kasance wakilin gidan gwamnati na gidan rediyon tsawon shekaru biyar.

”Abbas ya kasance majagaba a gidan rediyon Rahama Radio Kano daga 2011 zuwa 2012” ”Ya kuma kasance mai gabatar da labarai a gidan rediyon Vision FM kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum tare da kafafen yada labarai na kasa da na duniya a ciki da wajen Najeriya”.

Alfijr Labarai

”Abbas Yushau Yusuf kuma ya kware a tarihin siyasa da na soja a Najeriya kuma yana da gogewar koyarwa da hidimar al’umma

Yanzu haka Abbas shine ma mallakin jaridar Nigerian Tracker wanda ake wallafata a yanar gizo

Slide Up
x