Wani Jariri Da Mutane 4 Sun Sake Mutuwa A Hatsarin Kwale-kwalen Da Aka Yi A Jigawa

Alfijr ta rawaito Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wani jariri dan wata bakwai da mata hudu a wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Guri.

Alfijr Labarai

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Lawan Shiisu, ya tabbatar da faruwar lamarin a Dutse ranar Laraba.

A ranar Talata da misalin karfe 6 na yamma, bayanai da muka samu sun nuna cewa a ranar da misalin karfe 4:30 na yamma wasu mata hudu da yaro daya suka hau kwalekwale daga Nguru Yobe zuwa kauyen Adiyani da ke karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa.

Abin takaici, kwalekwalen ya kife kusa da inda suke.

Direban ya yi nasarar tserewa da ransa, yayin da fasinjan ya nutse a ruwa,” in ji Shiisu.

Ya ce nan take masu nutsewa a yankin suka yunkuro domin ceto fasinjojin, inda suka debo gawarwakin.

Alfijr Labarai

Shiisu ya ce an kai gawarwakin zuwa asibitin Adiyani kuma Likitan ya tabbatar da mutuwarsu, sunayenya bayyana sunayen wadanda wa suka mutun sune Oneyaniwura Kasagama mai shekaru 50 da Lafiya Bulama mai shekaru 40 da Badejaka Kasagama mai shekaru 40 da Gimto Kasagama mai shekaru 40 da Mai Madu Bulama jariri dan watanni bakwai.

PPRO ya ce wadanda abin ya shafa dukkansu mazauna kauyen Adiyani ne, inda ya kara da cewa an fara gudanar da bincike kan lamarin.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *