Tinubu Ya Bada Naira Miliyan 50 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jigawa

Dan Takarar Shugabancin kasa a Jam’iyyar APC A Jihar, Bola Tinubu ya bada gudunmawar naira Miliyan 50 Ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Jigawa.

Alfijr Labarai

Ya sanar da bayar da tallafin ne jim kadan bayan ya mika ta’aziyyarsa da Gwamna Muhammad Badaru, a Dutse ranar Talata.

Tinubu ya bukaci addu’o’in kawo karshen bala’in ambaliyar ruwa a jihar da ma kasa baki daya.

Ya ce, “Duk da cewa na yi addu’a ga wadanda abin ya shafa ta hannun gwamnan ku, amma na ji cewa na zo da kaina domin in jajanta muku yana da muhimmanci.”

Dan takarar ya samu rakiyar gwamnan jihar Filato Simon Lalong da shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu da shugabar mata ta jam’iyyar APC ta kasa Dr Betta Edu da tsohuwar shugabar hukumar EFCC Malam Nuhu Ribadu da sauran gaggagaggan jam iyyat.

Alfijr Labarai

Ana nasa bangaren Gwamna Badaru ya ce, ziyarar ta Tinubu ta kawo taimako ga wadanda ambaliyar ta shafa.

Ya ce, “Tunbu ya kira ni ya jajanta min a lokacin da aka samu ambaliya ta farko a Kafin-hausa, ya sake kira lokacin da lamarin ya faru a Hadejia, Gumel da Malammadori.

“Har ila yau, makonni biyu da suka gabata, an samu irin wannan lamari a Birnin-kudu, Gwaram da Dutse, daidai Karnaya nan ma ya kira, amma saboda jin kansa sai da ya bar duk abinda yake ya tako ya zo da kafarsa garemu

Slide Up
x