Wasu Gungun Yan Fashi Sun Fasa Bankuna Sun Kwashe Kudade A jihar Kogi

Alfijr ta rawaito wasu gaggan ‘yan fashi da makamai sun yi Dirar Mikiya akan bankunan Zenith Bank, First Bank da kuma UBA da ke karamar hukumar Ankpa jihar Kogi.

Alfijr Labarai

Al amarin ya faru ne a yau Talata da rana, yayin da barayin suka yi awon gaba da makudan kudaden, yayin da ‘yan fashin suka zo da wasu kananan motoci da babura da bas-bas, suka yiwa bankunan karkaf, hadi da masu POS dake daura da bankunan, in ji wata majiya.

‘Yan fashin sun dira ne da manyan Bindigun, sun kuma dau lokaci suna barnar, bayan kammalawa suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi har su tsere abin su ba a samu nasarar kama ko guda ba tare da kama ko guda daya daga cikin su ba.

Alfijr Labarai

Majiyar tace, jami’an tsaro ba su sami isa wajen ba har sai bayan sun gama sun watse suka iso.