Wata Sabuwa! Ƴan ƙungiyar Ysaherun IPOB sun fille kan ɗan majalisa

Alfijr

Alfijr ta rawaito wasu ƴan bindiga da a ke kyautata zaton ƴan haramtacciyar ƙungiyar IPOB ne sun cire kan wani ɗan majalisar dokokin Jihar Anambra, Dakta Okechukwu Okoye, bayan sun yi garkuwa da shi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne ƴan bindigan su ka sace ɗan majalisar da ake kira “Okey Di Okay” da ke wakiltar Aguata ta arewa, mazaɓar gwamnan Anambra, Farfesa Chukwuma Chukwuma Soludo.

Bayanai sun ce an tsinci kan ne da aka fille a gefen hanya tare da wata wasiƙa a yankin Amichi a Anambra

Alfijr

Rundunar ƴan sandan Anambra cikin wata sanarwa game da al’amarin ta ce a yayin gudanar da bincike wasu mutane sun tsinci gawar mutum ba kai, wanda aka tantance gawar ɗan majalisar ce Hon Okechukwu Okoye.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta wallafa a shafinta

Slide Up
x