Alfijr ta rawaito Ƴan bindiga sun harbe wani Inyamiri ɗan kasuwa, mai suna Ifeanyi a unguwar Sabongari a Jihar Kano.
Alfijr Labarai
Lamarinya faru ne ranar Asabar da ƙarfe 8:45 na dare a kan Titin France da ke Sabongari a cikin birnin kano, kusa da Kantin Azubros Kano.
Shaidun gani da ido sun ce da isar ƴan bindigar wajen, sai suka bude masa wuta, inda ya mutu nan-take ya ce ga garinsu can, su kuma su ka tsere.
Marigayin wani shahararren mai sayar da batira ne a Sabongari
Bayan Faruwar lamarin mutane suna ta neman tsira wasu sun sami raunuka saboda gudun tsira da rai
Alfijr Labarai
Za ku ji mu da kakakin rundunar ƴan Sandan jahar Kano domin jin cikakken bayani