Buhari Ya Tumbuke Shugaban Hukumar Kula Da Tsarin Raba Lamuni Na Ayyukan Gona (NIRSAL)

Alfijr ta rawaito wani bincike da aka gudanar kan yadda Nirsal ya lamunce bayar da rancen biliyoyin Naira na wasu kamfanoni masu zuba jari don noma hekta 20,000 na alkama na noman rani a Kano da kuma Jigawa bisa zargin karkatar da kamfanonin, tare da jami’an NIRSAL.

Abdulhameed ya musanta zargin yana mai cewa wasu marasa daraja ne suka kitsa hakan, domin bata masa suna da kungiyar.

Sai dai bayan rahoton, jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) sun gayyace shi da wasu jami’an NIRSAL domin yi musu tambayoyi kan rawar da suka taka a badakalar ayyukan alkama baya ga EFCC, ICPC da ‘yan sanda sun kaddamar da bincike a kan lamarin.

Wasu majiyoyi na cikin gida da suka tabbatar da faruwar lamarin sun ce biyo bayan umarnin da fadar shugaban kasa ta bayar, an kori MD din ne da yammacin ranar Alhamis din da ta gabata, aka kuma fitar da shi daga harabar jim kadan bayan ya yi wa ma’aikatan jawabi a takaice.

Duk da cewa har yanzu ba a mika shi a hukumance ba, wata majiya da ba ta so a bayyana sunanta ta ce an bukaci hukumar NIRSAL ta ba da sunan mukaddashin MD.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *