Gwamnatin Nijeriya Na Shirin Hana Cin Ganda A Faɗin Kasar

Alfijr ta rawaito gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa ta na shirin yin wata doka da za ta hana cin ganda a faɗin ƙasar.

Alfijr Labarai

Darakta Janar na Cibiyar Fasahar Kimiyya da Sarrafa Fatun Dabbobi, NILEST, Muhammad Yakubu ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja.

Ya bayyana cewar dokar ta zamo dole domin a farfaɗo da harkar sarrafa fata a faɗin ƙasar nan tare da farfado da kanfanunuwan sarrafa fata a kasar nan.

A cewar sa, dole ne gwamnati ta hana cin ganda, wacce ba ta da wani amfani wajen gina jikin ɗa’adam.

Alfijr Labarai

Ya ƙara da cewa hana cin gandar da farfaɗo da kamfanunuwan sarrafa fata zai bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce akwai lokacin ma da a ka taɓa tura ƙudurin a majalisa kuma an tattauna a kansa amma ban san ya a kai a ka ajiye shi ba.

“Idan a ka tabbatar da dokar a majalisa, to tabbas za ta farfaɗo da kamfanunuwan sarrafa fata a ƙasar nan,” in ji shi.

Daily Nigeria

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *