NDLEA, Ta Gurfanar Da Wani Matashi Ɗan Shekara 19, Abdullahi Aliyu, Gaban Kuliya

Alfijr ta rawaito hukumar sha da hana Fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa a ranar Juma’a, ta gurfanar da wani matashi mai suna Abdullahi Aliyu dan shekaru 19, a gaban wata babbar kotun tarayya dake Lagos bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.

A cikin tuhume-tuhume biyar da ke da alaka da safarar miyagun kwayoyi ba bisa ka’ida ba, Lauyan hukumar ta NDLEA, Mista Lambert Nor, ya yi zargin cewa Aliyu ya aikata laifin ne a ranar 13 ga Oktoba a kasuwar Alaba Rago da ke Ojo, Lagos.

Ya yi zargin cewa an kama wanda ake zargin da 1.2kg na Tramadol, 32g na Rohypnol da 2kg na Diazepam.

Hukumar NDLEA ta ce an ware magungunan a matsayin haramtattun kwayoyi da aka haramta a karkashin dokar NDLEA.

Laifin ya saba wa tanadin sashe na 11 (c) na dokar NDLEA mai iyaka N30 na dokar tarayya ta 2004.

Dokar ta tanadi hukuncin daurin rai da rai idan aka same shi da aikata laifin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *