Wata Sabuwa! Kotu Ta Bada Umarnin Tsare Shugaban Hafsan Sojin Kasa

Alfijr ta rawaito Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Minna, babban birnin jihar Neja, ta bayar da umarnin a kama shugaban hafsan sojin kasa, Janar Farouk Yahaya bisa laifin wulakanta Umarnin Kotu

Mai shari’a Halima Abdulmalik, wacce ta bayar da sammacin kuma ta jagoranci shari’ar, ta ce wannan umarni ya biyo bayan sanarwar da aka gabatar a gaban kotu bisa kin bin doka arba’in da biyu na dokar farar hula ta babbar kotun jihar Neja ta shekarar 2018.

Alkalin kotun ya yanke hukuncin cewa umarnin na tafiya ne a kan Yahaya, bisa umarnin ci gaba da tsare shi a gidan yari na Minna saboda takaddamar umarnin kotu a ranar 12 ga Oktoba, 2022.

Ya kara da cewa COAS zai ci gaba da kasancewa a gidan yari har sai an wanke shi daga raini.

Hakazalika, Alƙalin ya bayar da umarnin kama kwamandan horar da koyarwa na Minna, Manjo Janar Olugbenga Olabanji, tare da daure shi a gidan yari bisa irin wannan laifin.

Daga nan sai mai shari’a Abdulmalik ya dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Disamba.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki bayan da wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta yanke wa Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Baba hukuncin daurin watanni uku a gidan yari saboda ya ki bin umarnin kotu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *