Dokokin Qatar Sun Taimaka Wajen Dakile Faruwar Barna A Kan Mata

Alfijr ta rawaito wata fitacciyar ƴar gwagwarmaya kuma mai kwallon kwallo ta bayyana abin da ta gani a ƙasar Qatar.

Ellie, ‘yar kasar Ingila ta ce dokokin da aka sa a Qatar sun taimaka wajen dakile faruwar barna sosai kan mata

Ta kara da cewar ta samu natsuwar kallon kwallo fiye da yadda take kallo a kasar Ingila, inda ake hantarar mata, in ji Ellie.

Wasan da ake bugawa na gasar cin kofin duniya a kasar Qatar ya jawo cece-kuce tun bayan haramta wasu abubuwa da dama na rashin da’a, amma hakan ya ba maza natsuwa da koyar da darasi ga masu hantarar mata a filin kwallo a sauran kasashen duniya.

Ellie Molloson, ‘yar shekaru 18 mai goyon bayan kulob din Nottingham Forest kuma ‘yar fafutukar samar da tsararren wuri ga mata a filin kwallo ta ce da fari ta ji tsoron zuwa kasar domin goyon bayan Ingila a wasa ‘World Cup’ na bana.

Sai dai, a cewarta, ta ga sabanin haka, domin bata taba tsammanin samun natsuwa da kwanciyar hankali gami da rashin hantara daga maza ba a filin kwallon.

“Ban yi tunanin zan kasance cikin aminci ba a nan.”

“Sai kuma gashi, ban samu wani kira na batsa ba ko martani mara dadi ba da watakila zan iya samu a Ingila ba.

“Sun kasance masu matukar karbar baki da karimci.”

Ms Molloson dai ke jagorantar wani gangamin nemawa mata ‘yanci a filin wasan kwallon kafa da takin HerGameToo domin gangamin wayar da jama’a kan hantarar mata a filayen kwallon kafa.

Ta tafi kasar Qatar ne tare da mahaifinsa da kuma mai kula da lamurranta, inda ta bayyana cewa, kallon kwallon kafa ga mata a Qatar ya fi kallonsa a Ingila.

Shi kansa mahaifinta da ya zo kasar domin ba ta kariya cewa ya yi:

“Na fito ne musamman domin na kula da ita Ellie amma maganar gaskiya yanzu babu bukatar na nuna wata damuwa.”

Kwallon kafa na daya daga abubuwan da ke da muhimmanci a nahiyar Turai, musamman kasar Ingila, an dauko batutuwa da suka shafi shan barasa a filiyen kwallo, rahoton Financial Times.

Masu kallo da dama suna da yakinin cewa, haramta shan giya ne ya jawo wasannin ke tafiya daidai ba tare da hantarar mata ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *