Sama Da Lita 20,000 Na Man Dizal Ya Ƙone Yayin Da Gobara Ta Kama Tankuna Biyar A Kano

Alfijr ta rawaito Wata gobara ta kone wani gini da bai kammala ba da ake amfani da shi a matsayin wurin ajiyar man dizal, inda ta kone tankokin man dizal guda biyar dauke da lita 20,400 a unguwar Farawa Kwanar Yashi da ke cikin birnin Kano.

A cewar hukumar kashe gobara ta jihar, lamarin ya faru ne a ranar Talata, 7 ga watan Disamba, 2022, sakamakon tartsatsin wutar lantarki daga wani injin janareta da ake amfani da shi wajen loda man dizal daga tankokin dizal zuwa wasu tankunan saman.

Kakakin hukumar a jihar, SFS Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce mutane uku ne suka makale a cikin mummunan lamarin amma duk an ceto su da ransu kuma an garzaya da su asibiti domin yi musu magani.

Ya ce dakin nasu ya samu kiran gaggawa daga ma’aikatan da suka kai rahoton bullar gobarar a Kangon Saminu Farawa da ke hanyar Kwanar Yashi Maiduguri Roda da misalin karfe 00:29 na safe.

“Da isar su, sun gano cewa wani gini da bai kammala ba na kimanin 200 x 200 da aka yi amfani da shi a matsayin wurin ajiyar man diesel, kimanin tankokin dizal guda biyar dauke da kusan lita 20,400 na dizal, inji Lifan daya da janareta masu daukar aiki guda uku.

“Saminu ya kara da cewa namijin kokarin da mutanen mu suka yi, mun samu nasarar shawo kan lamarin tare da ceto tankunan man diesel guda uku, da wasu tankokin guda 9 tare da hana wutar bazuwa zuwa wasu wuraren.

Ya kara da cewa, “Yayin da mutane uku da suka makale, wato Mai Daura Sadi mai shekaru 24, Hassan Sadi, da Iliyasu Sadi kimanin shekara 25, an ceto su da ransu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *