CBN Ya Bayyana Yawan Kuɗin Da Za’a Iya Cirewa A Banki Da POS

Alfijr ta rawaito Babban bankin Najeriya CBN ya fitar da sababbin dokoki na hada-hadar kuɗaɗe a bankunan ƙasar.

Sanarwar da ya fitar ranar Talata, CBN ya taƙaita yawan kuɗade laƙadan da ƴan ƙasar za su iya cirewa daga asusun ajiyarsu na banki.

Wannan sanarwa na zuwa ne mako biyu bayan da Shugaba Buhari ya ƙaddamar da sabbin takardun naira da aka sabunta.

Sabbin matakan da CBN ɗin ya fitar a ranar Talata sun haɗa da:

1. Yawan kuɗin da mutum ɗaya zai iya fitarwa a banki a sati shi ne naira 100,000 yayin da kamfani zai cire naira 500,000 ne kawai a sati.

Idan mutum na son cire kuɗin da ya fi wannan adadi yawa to sai an caje shi kashi biyar cikin 100 ga mutum da kashi 10 cikin 100 ga kamfani na yawan kudin da zai cire.

2. Duk wanda ya je banki cire kudin da suka haura naira 50,000 da caki na banki da wani ya rubuta masa, to ba za a ba shi kudin ba. Yayin da dokar cire kuɗin da suka kai naira miliyan 10 ta amfani da caki a tsakanin bankuna daban-daban tana nan a yadda take.

3. Yawan kudin da mutum zai iya cirewa ta hanyar amfani da na’urar cire kudi ta ATM a sati kuwa shi ne naira 100,000, wato yawan abin da za a cire a ranar naira 20,000 ne kacal.

4. Takardun kudin naira 200 kawai bankuna za su dinga lodawa a cikin na’urar ATM.

5. Idan a wajen masu amfani da na’urar POS ne kuwa, naira 20,000 ce yawan kudin da mutum zai iya cirewa.

6. A yanayin da ake da tsananin buƙata kuwa da ba zai wuce sau ɗaya a wata ba, inda ake buƙatar cire kuɗin da yawansu ya fi wanda aka ƙayyade don wani dalili mai ƙarfi, to abin da za a bari mutum ya cire ba zai haura naira miliyan biyar ba, idan kuma kamfani ne to ba zai haura naira miliyan 10 ba.

Sannan a hakan ma sai an caji kashi biyar cikin 100 na yawan kudin ga mutum, da kashi 10 cikin 100 ga kamfani na yawan kudin da za a cire.

A cikin sanarwar, CBN ya ce, ga dukkan mai son yin amfani da doka ta shida, to zai ya bi waɗannan ƙa’idojin na ƙasa, don tare da sanya su a shafin CBN da za a ƙirƙira saboda hakan:

Ka tanadi katin shaida kamar katin ɗan ƙasa ko fasfon tafiye-tafiye ko kuma lasisin tuƙi.

Lambobi na musamman na banki wato BVN

Cikakken sanya hannun mai cire kuɗin

Samun amincewar babban jami’i don cire kudin a inda ake buƙatar hakan

Amincewa a rubuce daga wajen shugaban bankin don ba da damar cire kudin.

A yayin ƙaddamar da sabbin kuɗaɗen ranar 23 ga watan Nuwamban 2022, Shugaba Buhari ya ce sababbin takardun kuɗin za su taimaka wa Najeriya ta wajen warware matsaloli da dama da suke addabar ƙasar.

Dama tun a watan Oktoban da ya gabata CBN ya sanar da matakin sauya fasalin kuɗaɗen ƙasar, tare da umartar mutane da su mayar da tsofaffin kudaɗen banki don sauya musu da sababbi.

CBN, ya ce idan mutane suka mayar da kudaden ba tare da bata lokaci ba, to za su iya samun musayar kudinsu a kan kari.

BBC Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Slide Up
x

3 Replies to “CBN Ya Bayyana Yawan Kuɗin Da Za’a Iya Cirewa A Banki Da POS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *