Kotun Koli Ta Musanta Cewa Hukumar DSS Na Binciken CJN

Alfijr ta rawaito Kotun koli a yammacin ranar Talata a Abuja, ta yi watsi da wata jita-jita da ake yadawa cewa babban jojin Najeriya, CJN, Olukayode Ariwoola ya gurfana a gaban hukumar tsaro ta kasa (DSS) bisa zargin yin bayani dake nuna goyon bayan Gwamna Wike.

Kotun wacce itace mafi daraja a Najeriya ta kuma yi fatali da jita-jitar cewa alkalai biyar na kotun sun bukaci CJN ya yi murabus daga mukaminsa kan wannan batu.

A cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na kotun, Dr Festus Akande ya fitar, kotun kolin ta gargadi masu yada wannan jita-jita da su daina don amfanin kansu.

Kotun kolin ta mayar da martani ne ga wani labari da wata kafar yada labarai ta yanar gizo mai suna “People’s Gazette” ta buga, inda ta ce hukumar DSS tana bincikar Mai shari’a Ariwoola bisa zarginsa da furucin siyasa a Fatakwal a wani taron jama’a.

Sanarwar ta kara da cewa “Mun karanta wani labari cikin damuwa da kaduwa mai dauke da taken da wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta wallafa, “People’s Gazette,” tana zargin cewa Hukumar DSS tana bincikar Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, bisa kalaman da ya yi a ‘Port Harcourt wajen wata liyafa a jihar da kuma cewa ‘Alkalan Kotun Koli guda biyar suna kira da ya yi murabus.’

“Kamar yadda sanarwar manema labarai da muka yi a baya mun karyata wannan labari da bashi da tushe.

Kotun koli na ganin cewa wannan wata manufa ce da wasu suke son amfani da ita wajen samun karɓuwa da jan hankalin jama’a a daidai lokacin kasar nan ke tunkarar manyan zabuka a shekara mai zuwa.

“Muna so mu bayyana a sarari kuma ba tare da kuskure ba, cewa wannan wani sabon salo ne na yaɗa karairayi da wasu mutane da ba su da wata alaka da su suka shirya domin bata martaba da mutuntakar CJN da ma sauran jami’an shari’a wadanda ba za’a iya amfani dasu a sharioin da ka iya bujirowa bayan zabe ba.

“Ya bayyana a fili cewa wadanda ke da mugun nufi sun kammala shirye-shiryen kaddamar da dukkan hare-hare na hadin gwiwa a kan Jami’an Shari’a, tun daga CJN da nufin bata musu suna da kuma yi musu barazana don su yi shiru saboda munanan manufarsu.

“Tabbas, duk mai tunani ba zai sha wahala wajen fahimtar cewa wannan labari ƙarya ne mai cike da ruɗu da neman ɓata suna ba.

“A iya sanina, babu wani mai shari’a na koli da ya nemi CJN ya yi murabus, kuma babu wani mai shari’a na Kotun Koli da ya rubuta ko ya rubuta wata takarda ta nuna rashin amincewa.

“Alkalan kotun koli sun hada kai kuma suna goyon bayan CJN; kuma kamar yadda aka saba, duk suna aiki tuƙuru don tabbatar da adalci ba tare da tsoro ko son rai ba.

“CJN ko Alkalan Kotun Koli ko wasu Kotuna ba ‘yan siyasa ba ne, don haka babu wanda ya isa ya ja su zuwa siyasa ta kowace fuska.

“Shawarar da muke da ita ga wannan rukunin ’yan jaridar, wadanda jarin kasuwancinsu ya kasance yada labaran karya don haifar da tashin hankali da rashin gamsuwa, shi ne su sake tunani tare da shiga ayyukan da za su ciyar da kasa gaba. Kukan kurciya Jawabi ne inji masu iya magana” in ji sanarwar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *