Shifcin Gizo Ne Hana Bola Tinubu Bizar Shiga Kasar Amurka- APC

Alfijr ta rawaito Kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyya mai mulki APC Festus Keyamo ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a daren Asabar, 3 ga watan Disamba, 2022, sannan kuma ya fitar da hoton bizar Amurka na Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Karamin Ministan Kwadago da Aiki ya ce wannan jita-jita ba ta da tushe balle makama kuma aikin barna ne.

“Ga masu yin ƙarya da yada jita-jita marasa tushe game da an hana @officialABAT biza zuwa Amurka, ba ku bar mu ba tare da wani zaɓi ba face don nuna muku bizarsa ta yanzu wanda koyaushe ana sabunta shi tun da daɗewa.

Wannan jita-jita ta zo ne bayan da Tinubu ya sake shirya tafiye-tafiyen kasashen waje.

An shirya zai je Amurka, London, Faransa, da sauran kasashen Turai a wani bangare na yakin neman zabensa.

Majalisar yakin neman zaben ta ce an shirya tafiyar Tinubu zai fara ne a ranar 4 ga watan Disamba.

A halin da ake ciki kuma, Sanata Orji Uzor Kalu, jigo a jam’iyyar APC da ke cikin gwamnonin 1999-2007 kamar Tinubu, ya yi watsi da jita-jitar.

Orji Kalu ya yi ikirarin cewa ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta tabbatar masa da cewa za a karbi Tinubu a mako na uku na watan Disamba.

A wani sakon da ya wallafa a Facebook, ya rubuta cewa, “Yayin da zabe ke kara karatowa, ‘yan adawa za su kara yada labaran karya kan dan takararmu na shugaban kasa amma a ko da yaushe mu toshe kunnuwanmu da idanunmu.

Labarin cewa an hana Tinubu bizar Amurka karya ce kamar sauran labaran karya.

“Tinubu ya jinkirta tafiyar da kansa kuma ba a hana shi biza ba.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta tabbatar min da cewa za a karbi Tinubu a mako na uku na watan Disamba.

A matsayinsa na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarmu mai hazaka, za a yi masa kyakkyawar tarba a kasar Amurka.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *