Yadda Muka Kashe Kawata Muka Kuma Sayar Da Kanta Akan Naira 70,000 –

Alfijr ta rawaito Wani mutum ya furta a Ogun Ma’auratan da aka kama a ranar Asabar da ta gabata da laifin mallakar sassan jikin mutane a yankin Leme da ke jihar Ogun sun bayyana yadda suka kashe wata mata.

Ma’auratan, Kehinde Oladimeji mai shekaru 43 da matarsa ​​Adejumoke Raji mai shekaru 35, an kama su ne a ranar Litinin a hedikwatar ‘yan sanda ta jihar Ogun, Eleweran, Abeokuta.

Yayin da yake zantawa da manema labarai, mijin ya bayyana cewa matarsa ​​ta kashe kawarta ne kawai, wanda ta kai mata ziyara.

Ya ce matar ta kashe kawarta, inda ta yanka ta sannan ta raba sassan jikinta, wanda daga baya ‘yan sanda suka gano a cikin bokiti.

Oladimeji ya bayyana cewa an sayar da kan matar ga wani a Ibadan, babban birnin jihar Oyo akan kudi N70,000.

“Akwai wata rana matata ta gayyaci kawarta, wata mata zuwa gidanmu don ziyara.

A karo na farko da ta zo ranar Talata ne, ta zo a wannan ranar ta koma gida.

“Amma rana ta biyu da ta zo, ranar Alhamis ce.

A wannan ranar, matata ta dafawa matar, taliya da kwai, wanda ta ci.

Daga baya, matar ta shiga bandaki don yin wanka.

“Amma da dare ya yi a ranar, na tambayi matata yaushe kawarta za ta koma gida, amma matata ta ce ba ta da lafiya ne, kuma tana bukatar ta kwanta don ta sami ƙarfin jikinta.

A tsakar gida na zauna, amma da na dawo daki, sai na gane matata ta kashe kawarta kuma ta tsinke gawarta.

“Lokacin da na tambaye ta dalilin da ya sa ta yi hakan, sai ta gaya mini cewa matar ta yi mata laifi tuntuni.

Wanda ya sayi kan matar ya fito daga Ibadan, ne Sunansa Oluomo,” mijin ya bayyana.

Ya ce, “Ina da wani abokina a Ibadan, wanda aka fi sani da Omo Baale.

Ya ce mini yana bukatar sassan mutum, amma na ce masa ba ni da irin wannan alaka ko kuma wani wanda zai taimaka wajen samar ma shi.

Matata ta ji zancen kuma ta tambaye ni nawa ne mutumin zai biya na kan ɗan adam. Na ce masa a shirye yake ya biya Naira 70,000.

Ban taba sanin matata ta yanke shawararta ba.

“Kamar yadda kuke gani, ni ba mutum mai ƙarfi ba ne. Lokacin da lamarin ya faru, na so in kashe kaina.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *