Ganganci! Wata Ƴa Ta bankawa iyayenta wuta

Alfijr ta rawaito Rundunar ‘yan sanda a jihar Lagos ta fara gudanar da bincike kan halin da ake ciki game da yadda wata Mata Mai shekaru 52 ta bankawa mahaifinta Mai shekaru 85 da matarsa ​​mai shekaru 80 wuta.

Bayanan da suke fitowa suna nuna cewa wata mata mai shekaru 52 mai suna Aleremolen Izokpu ta bugar da mahaifinta mai shekaru 85 mai suna Pa Michael Izokou da matarsa ​​Priscilla ‘yar shekara 80, daga bisani Kuma ta banka musu wuta.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba a City Gate Estate da ke unguwar Lusada a Okokomaiko, a kan hanyar Lagos zuwa Badagry.

A cewarsa, an tabbatar da mutuwar dattijon a asibitin da aka kai su, yayin da matar tana can a sume.

Mista Hundeyin ya ce: “Bayanan da aka samu daga wajen Baturen Yan sanda na cajin ofis din Okokomaiko sun nuna cewa a ranar 01/12/22 da misalin karfe 09:00 na safe ne, wani ya kawo rahoto ofishin cewa a ranar 30/11/22 da misalin karfe 3:00 na rana, kanwarsa ta kirashi Mai suna Osemudiame Izokpu inda ta gaya masa cewa babbar Yar su mai suna Aleromolen mai shekaru 52 ta ba wa iyayensu miyagun kwayoyi wato Micheal Izokou mai shekaru 85 da kuma Priscilla Izokpu mai shekaru 80 sannan ta banka musu wuta a lokacin da suke barci.”

“Jami’an tsaro sun ziyarci wajen da al’amarin ya faru sannan kuma sun ziyarci asibitin da aka ajiye gawar mahaifin da kuma mahaifiyar da ke samun kulawa. Haka Kuma jamian sun dauki hotuna Kuma sun ajiye gawar a dakin ajiyar gawa na asibitin Badagry.

Haka kuma Mista Hundeyin ya kuma bayyana cewa, hukumar Yan sanda zata tashi tsaye wajen ganin ta kamo wanda ake zargi da ta gudu.

Daya daga cikin ‘yan’uwan wanda ake zargin Akugbe Izokou ne ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda bayan daya daga cikin kanwarsa ta sanar da shi ta wayar tarho.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Slide Up
x

One Reply to “Ganganci! Wata Ƴa Ta bankawa iyayenta wuta”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *