“Idan Mata Suka Hana Mazansu Aure, Za Su Nemi Na Banza” – Nwoko

Alfijr ta rawaito wani tsohon dan majalisa a Nijeriya Ned Nwoko ya koka kan yadda tarbiyya ta tabarbare a wannan zamanin.

Tsohon dan majalisar da ya auri tauraruwar fina-finan kudancin Nijeriya Regina Daniel na magana ne a zantawarsa da The Guardian ya ce muddin mata suka hana mazansu kara aure, to kuwa dole mazajensu su tsunduma neman mata a waje.

Nwoko da yanzu haka ke da mata shida ya bukaci maza a kudancin Nijeriya su yi koyi da mazajen arewaci wajen kara aure da zummar kawar da fasadi a yankin.

Attijirin da ke takarar Sanata a jiharsa ta Delta a PDP ya ce galibin maza a kudu na ikirarin samun nutsuwa da mace daya amma a zahiri suna da ‘yan mata masu yawa, ya kuma zargin cewa abin da mazan kudun ke kashewa kan ‘yan matan ya fi abin da suke kashe wa iyalansu.

Duten-Kura

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *