Ƴan Sanda Sun Damke Wani Da Ya Binne Jaririya Da Ranta A Jigawa

Alfijr ta rawaito yan sanda sun tono gawar wani jariri da aka binne shi da rai a karamar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 02/12/2022, da misalin karfe 2350 bayan wani Balaraba Shehu dan shekara 30 da ke kauyen Tsurma a karamar hukumar Kiyawa da ake zargin ta haihu tare da binne sabon jaririn.

Shiisu ya ce bayan da ‘yan sanda suka samu rahoton, an tattaro tawagar ‘yan sanda inda aka zarce zuwa wurin da aka aikata laifin.

Ya ce da isar su jami’an tsaro sun shiga aikin tare da tono sabon jaririn da aka binne a bayan gida.

Ya kara da cewa, an kama wanda ake zargin kuma an garzaya da jaririn zuwa babban asibitin Dutse, kuma likita ya tabbatar da cewa ya mutu.

Ya bayyana cewa binciken farko ya kai ga kama wani matashi dan shekara 25, Amadu Sale wanda aka fi sani da Dan kwairo na kauyen Akar da ke karamar hukumar Kiyawa wanda ake zargi da yin cikin da ba a so ba.

Sai dai wadanda ake zargin sun hada baki suka binne jaririn bayan haihuwa.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Jigawa, CP Emmanuel Ekot Effiom ya ba da umarnin a mika karar zuwa SCID Dutse, domin gudanar da bincike mai zurfi.

Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan bincike.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *